INEC Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci A Zamfara

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, a Jahar Zamfara ta shawarci fusatattun ‘yan siyasan da suke zargin jami’an hukumar da karban cin hanci a Jahar ta Zamfara, da su garzaya kotun sauraron kararrakin zabe.

Shugaban sashen wayar da kan al’umma a kan zaben na Jahar Zamfara, Garba Galadima, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Gusau.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya kawo rahoton cewa, gamayyar Jam’iyyun siyasa tara a Jahar sun yi zargin cewa, hukumar ta yi aiki ne domin samun nasarar jam’iyyar ta APC a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Jahar.

Gamayyar jam’iyyun sun yi kiraa  da a hanzarta tsige Kwamishinan zabe na Jahar, da duk shugabannin hukumomin tsaro na Jahar kafin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisu na ranar 9 ga watan Maris.

Kakakin gamayyar jam’iyyun, dan takaran gwamna a karkashin jam’iyyar APGA, Sani Shinkafi, ya shaidawa taron manema labarai cewa, gammayar jam’iyyun ba su da fatan samun adalci daga jami’an hukumar zaben da kuma hukumomin tsaron da ke Jahar.

Da yake kare kan shi, Galadima yace  jinkirin da aka samu wajen raba kayan zaben ya faru ne saboda jinkirin umurnin hakan da aka samu da kuma umurnin kotu na cewa, jam’iyyar APC wacce da farko ba ta a cikin takardun zaben, sai daga baya ne aka yi umurnin a shigar da ita.

“Sai da muka musanya takardun zaben da muka aike da su ba dauke da sunayen ‘yan takaran APC ba, muka sake lodawa wasu motocin takardun zaben da suke dauke da sunayen ‘yan takaran na jam’iyyar ta APC. “Motar karshe da ta tashi daga babban bankin kasar nan a ranar Juma’a ta nufi Tsafe, ta tashi ne da misalin karfe 12 na rana.

Hakan ya shafi rashin fara zaben da wuri. Bayan wannan dalilin na rashin isowar kayan zaben a kan lokaci, mun fuskanci matsalar na’urar tantance masu zaben a wasu rumfunan zaben wadanda aka soke zabukan na su a kan hakan, ga kuma matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Mada, da rikicin da aka yi a wasu rumfunan zaben. “Kan haka, hukumar zaben ta yanke shawarar gudanar da zaben a ranar 24 ga watan na Fabrairu, a wuraren da abin ya shafa, domin baiwa masu zaben hakkin su na yin zaben.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: