Jami’an tsaro sun bincike ne – Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya a   karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami’an tsaron kasar sun bincike shi ranar Lahadi jim kadan da dawowar sa babban birnin tarayyar  ta Abuja,

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya dawo kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwanaki tare da wasu abokan siyasa da mukarrabansa.

Duba da cewar baiyi  yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka bincike shi  din ba.

Sai dai har yanzu  hukumomi ba su ce wani abu kan batun bincikar nashi ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jami’an tsaron sun dauki matakin yin haka ne da zummar yi masa barazana.

A cewarsa, “Na iso Abuja da safiyar nan inda jami’an tsaro suka bincike ni da zummar yin barazana ga ni da  ma’aikatana.”

“Na sha alwashin gina Najeriya yadda babu wani jami’in tsaro da ake biyansa da kudin ‘yan kasar domin ya kare su zai rika yi musu barazana,” in ji Atiku.

Rahotanni sun ce Alhaji Atiku Abubakar ya je Dubai ne domin hutawa da kuma gudanar da taruka na siyasa gabanin soma yakin neman zabe ranar 13 ga watan Nuwamba.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: