Jami’an tsaro sun rufe kasuwar Wuse.

Da misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata  Charly Boy yaje kasuwar Wuse don neman izini a bashi damar gudanar da zanga-zanga kan shugaban kasa Buhari a kan ya dawo gida daga birnin London inda yake jinyar rashin lafiya ko kuma yayi murabus.

Rashin samun izini daga shugabannin kasuwar ne yasa shida mukarraban sa suka kutsa kai don yin zanga zanga inda matasan kasuwar suka farmasa don nuna rashin goyon bayan su akan kudirin sa cewar Buhari ya sauka daga kan mulki ko ya dawo gida najeriya. Shahareren mawaki, Charles Oputa, wanda aka fi sani da Charley Boy, wanda shine jagaba wajen zanga-zangar kira da shugaba Buhari ya dawo gida ko ya sauka daga kan mulki.

. A satin da yagabata, jami’an tsaro suka tarwatsa mawakin da magoya bayan sa saboda zanga-zangar da suke yi a harabar majalisar tarayya (Unity fountain) dake Abuja. “Charley Boy ya shigo cikin kasuwar ne da wasu yan jaridu domin yin zanga-zangar .“Saura kadan su hallaka shi, saboda abun yafi  karfin jami’an tsaron da su ke tare da shi.” Jami’an tsaro sun samu nasarar kwantar da tarzomar ne lokacin da suka fara harbe-harbe da jefa wa matasan barkonan tsohuwa.

 

You might also like More from author

Comments are closed.