Jam’iyyar APC tsintsiya madauri daya ce – Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa kwamared Adams Oshiomhole, yace  dukkanin dan jam’iyyar APC ya zama cikin shiri game da hade kawuna wajen ganin an samu nasara cin zaben 2019, duba da cewa lokaci kalilan ya rage na yin zaben.

Adams Oshiomhole ya bayyana hakan ne a taron da ya shugabanta a babban offishin jam’iyyar ta APC dake babban birnin tarayya Abuja a yau Al’hamis 6 ga watan Disamba 2019.

yan takarkarun gwamnan, shuwagabanin  jam’iyya, sakatarorin jam’iyya tare da masu ruwa da tsaki a APC  na jahohi 36 a fadin  kasar ta Najeriya suka hallata taron, inda Adams ya kara da cewa dukkannun su  yana da kyau su karawa juna sani, Saboda tantacce manyan shuwagabanin su ko a ina ne.

Yayi kira ga duk wani mai ruwa da tsaki na APC  da ya zama tsintsiya daya madauri daya

A karshe yace a yi kokarin hada kai dan ganin a zauna lafiya domin  tafiyar da yakin neman zabe ta sauki da lumana ba tare da tashin hankulan al’umma ko wanne yankin da jahohi na kasa baki daya ba.

You might also like More from author

Comments are closed.