Jam’iyyar MRDD ta bukace a dakatar da zaben jahar Adamawa

Bayan wata babbar kotu a jahar Adamawa ta ba da umarnin dakatar da zaben jahar da za a kammala, hukumar zaben ta INEC reshen jahar ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar hukuncin.

Yanzu haka Jam’iyar MRDD ta garzaya babban kotun jahar ta Adamawa, dan a dakatar da zaben jahar da za’a gudanar na ranar 23 ga wata Maris bisa dalilin zargin da suke yi na rashen saka alamar jam’iyyar azaben gwamna da aka gudanar na ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019

Hakan yasa kotu ta umarci hukumar zabe mai zaman kan ta wato INEC da ta dakatar da zaben har sai an yanke hukuncin da yaka mata.

Sai dai kuma a taron manema labarai da hukumar ta kira, kwamishinan hukumar zaben jahar, Barrista Kassim Gana Gaidam, ya ce sun samu umarnin kuma hukumar a shirya take  gurin  kalubalantar umarnin a gaban kotu.

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyar PDP, Ahmad Umaru Fintiri, shi ne ya ke kan gaba a zaben da aka yi, inda ya yiwa gwamnan jihar na  jam’iyar APC fintinkau da kusan kuri’u dubu talatin da doriya.

Sakataran Tsare-Tsare na jam’iyyar APC a jahar Adamawa, Hon. Ahmad Lawal, ya ce sun shirya shiga wannan zabe muddin kotu ta ce a gudanar da shi, kuma a shirye su ke domin su ga sun lashe zaben gwamnan da za a kammala.

Yanzu haka dai jam’iyar PDP ta samu yawan kujeru 11 cikin 25 na kujerun majalisar dokokin jihar, inda itama jam’iyar APC da ada kujerunta ne baki daya itama ta sami kujeru 11.

Yayin da sabuwar jam’iyar ADC ta samu kujera daya, sannan kuma za’a kammala na saura kujeru biyu a wannan asabar.

A yau Alhamis 21 ga watan Maris 2019 ake shirin fara sauraren karar.

 

You might also like More from author

Comments are closed.