Jan aiki ne a gaban sabon shugaban kasar Sudan

Shugaban majalisar sojoji da ke mulkin Sudan ya yi alkawarin tsige gwamnatin da sojojin suka yi wa juyin mulki kwanaki  da suka gabata.

A yayin da sabon shugaban kasar Sudan Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman yake jawabi a tashar talabijin, Burhan ya sanar da garambawul ga ma’aikatun gwamnati, kuma ya soke dokar hana fita cikin dare kuma ya umarci a sako dukkan fursunonin siyasa da tsohuwar gwamnati ke tsare da su.

A halin da ake ciki, masu zanga-zanga sun cigaba da zama a harabar shedikwatar sojojin kasar.

Masu zanga-zangar na neman a kafa gwamnatin da fararen hula ke jagoranta nan take, kuma sun lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai sun cimma muradunsu.

Janar Burhan ne ya maye gurbin shugaban da ya jagoranci juyin mulkin da ya hambare Omar al-Bashir, wanda kuma yayi murabus bayan kwana daya a kan mulki.

Sabon shugaban ya rushe dukkan gwamnatocin lardunan kasar kuma ya yi alkawarin kare hakkin dan Adam.

A cikin jawabin nasa, ya rika amfani da kalamai masu nuna yana son sasantawa da masu zanga-zangar domin su taimaka wajen ganin na dawo da zaman lumana a kasar.

Jawabin sabon shugaban ya biyo bayan ajiye aikin shugaban hukumar tsaro ta cikin gida Janar Salah Gosh, wanda shi ma ya biyo bayan saukar da ministan tsaro Awad Ibn Auf yayi bayan ya hambare gwamnatin Omar al-Bashir.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: