Jarimin Kannywood Nuhu Abdullahi ya sayi motar miliyan 12

Motar da  shaharanren  jarimi  Nuhu Abdullahi ya saya ta janyo cece kuce a kannywood

A yayin da Nuhu Abdullahi ya saka sabuwar motar da ya siya a shafin sa na Instagram kamar yanda mutane da dama suke yi idan abun farin cike ya same su ,ko  kuma sabanini haka, masamman ma jaruman fina-finan kannywood, Hollywood, Bollywood da dai sauran su.

Duba dace wa hakan ya zama jiki ga al’umma baki daya ba ma jarumai ba.

Sai dai a na ta cece kuce akan ina jarumin, Nuhu Abdullahi ya samu kudin  siyan motar mai kirar Mercedes C300 2016, wacce ta kai kimanin naira miliyon goma shabiyu da dubu dari (N12,100,000) duba da cewa a fadin masana’antar ta kannywood babu wanda yake hawan irin kirar motar sai Naziru Ahmed wato sarkin wakar sarkin Kano Sususi Lamido Sunus na 11

Hakan yasa wasu da dama suke ganin cewa siyasar da ya shiga ne, ko kuma matsayin sa na  ambasadar FIRS​ ne ya bashi damar samun kudaden da ya sayi motar.

Sai dai jarumi Nuhu Abdullahi  ya shaida wa Oak TV Hausa cewa shifa Allah ne ya bashi damar  siyan mator kuma yana  kara godewa Allah duba da cewa yana kan bakan sa na neman halaliyar sa a ko wanda lokaci.

Nuhu Abdullahi ya kara da cewa shi bazai hana duk wani wanda zai yi magana ko ya fadi ra’ayin sa a   kan hakan ba, shi dai abuda ya sani hasada ga mai rabo taki ce kuma kulli yaumi a gurin Allah yake ruko, kuma ya san yana tare da Allah a koda yaushe.

 

You might also like More from author

Comments are closed.