Kalamun Shugaba Buhari Yankin Tafkin Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadi da su kara hada kai domin ganin sun magance matsalar tsaro a yankin.

Shugaban yayi magana ne a birnin Ndjamena na kasar Chadi a lokacin wani taro na musamman tsakanin shugabannin kasashen da ke cikin hukumar mai suna Lake Chad Basin Commission.

An kira taron ne sakamakon karuwar hare-hare da ake samu a yankin a ‘yan watannin nan, kuma shugaban na Najeriya ya nemi takwarorinsa daga Chadi da Nijar da Jamhuriyar Kamaru da su kara zage dantse wajen ganin sun dakile mayaka, musamman na kungiyar Boko Haram. Inda ya kara da cewa a wannan ya kamata a dau mataki na gaggawa

Ya kuma bayyana cewa yankin ya fuskanci karuwar hare-hare da suka janyo tabarbarewar tsaro, musamman ma a kan sansanonin sojoji daga kungiyar Boko Haram wadanda suka hada da satar mutane.

Shugaban ya kuma nemi shugabannin kasashen da suka halarci taron da su tashi tsaye wajen samar da ruwa ga tafkin na Chadi daga yankin Congo.

Shugaba Buhari ne ke jagorantar taron koli na shugabannin kasashen yankin tafkin na Chadi.

Manyan Shugabannin da suka halarci taron sun hada da Shugaba Idris Deby Itno na Chadi da Shugaba Mahamadou Issoufou Jamhuriyar Nijar da kuma Firai ministan Jamhuriyar Kamaru Philemon Yang, wanda ya wakilci Shugaba Paul Biya.

A sanarwar bayan taron da shugabannin suka fitar, sun jaddada cewa za su ci gaba da hada kai domin magance dukkan matsalolin ta’addanci da masu aikata manyan laifuka, har sai zaman lafiya ya dawo a yankin.

You might also like More from author

Comments are closed.