Kau da bara sai da hadin kan gwamnonin Najeriya- Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu  Buhari ya bayyana almajiranci a matsayin  hanyar da ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Buhari yayi wannan bayanin ne fadar sa a  lokacin da Kungiyar Likitocin Najeriya wato NMA da  suka  kai masa ziyarar ban girma.

Kakakin Shugaban kasan Femi Adesina, ya fitar da  sanawar da ke da cewa shugaba Buhari yace nauyin kawo karshen almajiranci ya na rataye ne a wuyan gwamnatocin jihohin Najeriya domin sai da hadin kan su za’a iya magance matsalar  barace-barace a kasar.

You might also like More from author

Comments are closed.