Khadija Bukar Abba Ta Yi Murabus Daga Mukamnin ta Na Minista

Uwargidan tsohon gwamnan jahar Yobe Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ta yi murabus daga mukaminta  na karamar ministan harkokin kasashen waje na  kasar Najeriya.

Hajiya Khadija Bukar tana daga cikin wayanda  za’a kara da ita a zaben majalisar wakilai da za a gudanar ranar 16 ga watan Feburairun 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Jaridar Punch ta ruwaito cewar hakan shine dalilin da yasa Khadija Bukar tayi murabus daga makamin  nata.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.