Kinsasan tawar Kwankwaso Da Ganduje barazana ce ga Jahar Kano

Sakamakon rashin jituwar da ake gani tana kara tsananta tsakanin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Ubangidansa a siyasance, Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Injiniyar Rabiu Musa Kwankwaso, yanzu haka wata kungiyar kiyaye hakkin dan Adam ta fara yunkurin sasanta aminan junan biyu, kungiyar ta samar da kwamitin da su ka dorawa alhakin sasanta jiga-jigan jam’iyyar ta APC a Kano.

Shugaban Kungiyar mai suna ‘Rigar ’Yanci’, Kwamared Mustapha Haruna Khalifa ya ce, ba zai yiwu manyan ‘yan siyasa irinsu Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Kano, su ci gaba da kawo rikice-rikice karshe har ta kai ga zubar da jini. Musamman ma bisa la’akari da kasancewar Kwankwaso da Ganduje jiga-jigai a siyasar Jihar Kano, saboda haka rashin daidaito a tsakanin mutanen biyu babban kalubale ne ga al’ummar jihar da ma Jam’iyyar ta APC, musamman mata da kananan yara.

Wannan dalili yasa wannan kungiya ta kafa wani kwamiti domin gayyato wadannan mutane biyu domin samun matsaya tare da dinke barakar dake neman kassara ci gaban da ake bukata a tsakaninsu, wannan yunkuri ci gaba ne babba hakan kuma zai samar da zaman lafiya a Jihar Kano.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: