Koh misis Ezekwesili zata iya karawa da Shugaba Buhari da Atiku?

Misis Obi Ezekwesili wacce take  jagorantar yakin neman  ceto ‘yan matan Chibok  276 daga makarantar ‘yan mata dake  garin Chibok ta arewacin Najeriya a shekarar 2014.

Tayi  mataimakiyar shugabancin babban Bakin Duniya, kuma taba rike mukamin ministar ilimi.

Ezekwesili mai shekara 55 wacce jam’iyyar ACPN ta tsayar da ita a matsayin yar takarar shugaban kasa, koh  zata iya kada shugaban kasa  Muhammadu Buhari na jam;iyyar APC mai shekara 75 tare dan takara a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar mai shekaru 72 daba da kawane yana da magoya baya masu yawa?

Wa’adin rajistar tsayawa takarar ya cika ne da karfe sha biyu na dare agogon Najeriya ranar Lahadi, kuma a kalla ‘yan takara tara ne a ke zaton sun mika takardunsu.

                                        

A taron da ACPN da  Misis Ezekwesili ta hallarta   ta bayana cewa   mazan da za ta fuskanta a zabensu  “wani rukuni ne na ‘yan siyasa da ke walagigi daga wanan rikici zuwa wanan rikici”,

Tana shirin fitowa a matsayin ‘yar takara mai adawa da masu rike da madafun iko, inda ta kira ‘yan siyasar da ke rike da kasar masu dagula al’amurra.

Sai dai a wani yunkuri irin na tsohon shugaban Amurka Barack Obama, jam’iyyar ACPN na yi mata lakabi da ‘yar takara mai cike da “buri”.

Misis Ezekwesili, mai shekara 55 na kokarin kyautatawa matasan kasar, inda ta ce mutanen da ke rike da madafun iko ba su fahimci sauye-sauyen da ke faruwa ba, musamman a fannin fasaha.

Fiye da kashi 50 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su kai shekara 30 ba.

“Ya za a yi a ce kasar da ke da yalwar miliyoyin matasa, masu jini a jika, da fasaha ta saki jiki?” Ta tambaya.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.