Kotu ta dakatar da tattara sakamakon zaben Bauchi

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato  INEC ta bi umarnin kotun tarayya na dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Bauchi.

Amma ana sa ran cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zabe na ‘yan majalisar dokoki na jahar.

Talata 19 ga watan Maris, wata babbar kotun tarraya a Abuja ta dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke Bauchi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Hakan yazo ne  a daidai lokacin da ake shirye-shiryen tattara sakamakon karshe na jahar, bayan da hukumar zabe a kasar ta bayyana zaben jahar a matsayin wanda bai kammala ba.

Wakilin jaridar Daily Trust John Chucks wanda ya halarci zaman kotun ya ce Mai shari’a Ekwo Ejembi ya ba da umarnin ne a ranar Talata, bayan jam’iyyar APC da Gwamnan jahar Mohammed Abubakar sun shigar da kara a gaban kotun.

A safiyar Talata dai dakin tattara sakamakon ya fara cika domin jaran fara tattara sakamakon sai dai aka ji kwatsam kotu ta dakatar da tattara sakamakon zaben.

A ranar Asabar ne hukumar INEC ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa ta ce gano akwai kuskure wajen lissafin kuri’un da aka soke a rumfuna hudu a karamar hukumar Ningi inda aka ce sun kai 25,330, maimakon 2,533 wadanda INEC din ta ce su ne alkaluma na gaskiya.

Hukumar ta ce a yanzu za a sake lissafi da alkaluma na gaskiya na kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi da suke 2,533.

 

You might also like More from author

Comments are closed.