Kotu ta haramtawa majalisa binkikar Ganduje

Kotun jahar Kano ta hana majalisar dokokin jahar  gudanar da bincike a kan wani bidiyo da ke nuna Gwamna Abdullahi Ganduje yana karbar wasu daloli da ake zargin cin hanci ne a gurin wayanda ba’a san su waye ba.

Wata kungiyar lauyoyi masu fafutukar kare demokuradiyya ne suka shigar da karar, inda suka kalubalanci majalisar cewa ba ta da hurumin gudanar da binciken.

Kotun wadda mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasi ya jagoranci zaman nata ta amince da bukatun da bangaren mai karar ya gabatar mata, ciki har da haramta wa majalisar gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje, kasancewar yana da rigar kariya, kuma ba aikin majalisar ba ne gudanar da bincike a kan miyagun laifuka.

Hakan yasa kotun ta jaddada cewa ‘yan sanda da hukumomi dangin EFCC, wato da ICPC, su ne kundin tsarin mulkin kasa ya dora musu alhakin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa Gwamnan, don haka kamata ya yi a tura musu hotunan bidiyon tun lokacin da aka same su, don su yi aikinsu.

 

You might also like More from author

Comments are closed.