Ku yafewa Yahaya Bello – Aisha Buhari da El’Rufa’i ga mutanen Kogi

Uwargidan shugaba Buhari wato Aisha Buhari ta bayyana cewar aikin tantance ma’aikatan gwamnati na jahar Kogi ne dalilin da yasa Gwwamna Yahaya Bello ya kasa biyan albashi a jaharsa.

Inda tace,ana kammala aikin tantancewar, ma’aikatan jahar suka fara samun albashinsu a kan lokaci kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakan yasa Aisha Buhari ta roki al’ummar jahar su yi wa Bello afuwa kan halin da suka shiga na matsi yayin aikin tantancewar, tare da rukar su manta da duk wani matsi da suka shiga a baya.

Aisha ta yi bayyana hakan ne a lokacin data ziyarci jahar kogi  wajen  taron yakin neman zaben na jam’iyyar APC a ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba 2019, jim kadan kuma gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya durkusa gaban al’ummar ya roki su yafe wa gwamnan. A yayin da ta ke jawabi ga mahalarta taron, Aisha Buhari ta ce, “Kamar yadda gwamnan jihar Kaduna ya durkusa ya roke ku nima ina so in ce al’umma su yafe abinda ya faru a baya su manta da shi.

“Kamar yadda aka sani, miji na ya saba magana a kan albashi. An dauki lokaci mai tsawo kafin aka tantance ma’aikatan Kogi sannan aka warware matsalar albashin. “Amma wannan karon, ku zabe shi domin ya cigaba da biyan albahsi a kan lokaci.”

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: