Kuyi sallar Idi a gida tare da iyakenku

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta ce bai kamata a yi taron Sallar Idi ba saɓanin yadda wasu jihohi ke bayar da damar yi.

Kwamitin fatawa na kungiyar karkashin jagorancin Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Alhusainy ya tatattauna tare da fito da matsayarsu game da sallar yayin annobar korona kamar haka:

Bai kamata a yi jam’in Idi a cikin birane da wajensu ba

Mutane su yi Sallar Idi a gida tare da iyalansu ko kuma mutum ya yi shi kaɗai idan babu kowa tare da she

a- Sallar Idi raka’a biyu ce tare da kabbara bakwai (7) a raka’ar farko haɗi da kabbarar farko, sannan a karanta fatiha da kuma wata sura – an fi son a karanta Suratul A’ala wato Sabbi

b- A raka’a ta biyu kuma za a yi kabbara biyar (5) sannan a karanta fatiha da kuma wata sura – an fi so a karanta Suratul Gashiyah wato Halataka.

Idan za a yi Sallar Idi a gida ba sai an yi huɗuba ba

Dukkanin abin da aka faka a sama daga mazahabar Imam Malik aka ciro su a littafin Mukhtasar

A jihohin da aka bayar da damar yin Sallar Idi, ya kamata a yi amfani da masallatan cikin unguwa idan ya zama dole. .
A bi sharuɗɗan da masana harkar lafiya suka bayar na saka takunkumi da wanke hannu da yin nesa-nesa da juna

Malamai su ji tsoron Allah su kiyaye harshe da kuma ayyukansu domin kare mutuncin addini da kuma Musulmai

Ranar Asabar ko Lahadi ake sa ran yin Idin karamar Salla, kuma tuni jihohi irinsu Kano da Borno da Jigawa da Adamawa da Gombe suka bayar da damar buɗe masallatan Idi domin gudanar da sallar da ake yi saboda kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.

Sai dai gwamnatin tarayyar Najeriya na korafi kan sassauta dokokin kulle da gwamnonin ke sassautawa a jihohinsu, inda ta ce “muna tufka jihohi na warwarewa” a yakin da ake yi da annobar korona a kasar.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: