Laffuzan Janar Buratai Ya Janyo Cece-Kuce Tsakanin jami’an Tsaro

Babban hafsan hafsohin sojojin Najeriya, janar Tukur Buratai, ya yi jawabi wajen wani taron bita da aka shiryawa dakaru,  a babban birnin tarayyar Abuja.

Janar Buratai ya ce “rashin kwazo dayin azama wajen yin fada, na wasu daga cikin hafsoshi da sojoji na daga cikin abubuwan dake haddasa musu koma baya a fafatawar da ake yi yanzu haka.”

Inda ya kara da cewa  ko da zagon ‘kasa da ake yi musu, akwai kuma tabbatattun shaidu dake nuna koma bayan da ake fuskanta a baya-bayan nada alaka da rashin kishin ‘kasa da kuma rashin kishin aikin soja.

Tuni dai wannan jawabi na janar Buratai ya haddasa cece-kuce tsakanin masana tsaro da kuma tsaffin jami’an tsaron.

Dakta Kabiru Adamu, na daga cikin wadanda ke ganin rashin dacewar jawabi na Buratai, inda ya ce ko da kuwa akwai matsalar tsaro bai kamata ba hafsan Soja ya fito ya yi irin wadannan kalaman ba a fili ba.

Sai dai kuma tsohon hafsa a rundunar sojan Najeriya, majo Shu’aibu Bashir Galma, na ganin maganar  da janar Buratai ya yi na bisa hanya idan akayi duba bisa ala’amuran

You might also like More from author

Comments are closed.