Litar mai fetur zai dawo naira 123 a Najeriya

Kamfanin man a kasar Najeriya ya rage fashin litar man fetur daga naira 125 zuwa naira 123.

Kamfanin ya umarci gidajen mai da su fara sayar da mai a kan sabon farashin daga ranar Litinin 1 ga watan Yunin, 2020.

Hukumar da ke kayyade farashin mai ta Najeriya ce ta sanar da sabon farashin man, wanda ta ce daga yanzu farashin litar mai ba zai wuce tsakanin  naira 121 da kobo hamsin zuwa 123.50 ba.

Kakakin hukumar, Mista Apolos Kimchi, ya shaida wa BBC cewa an rage farashin ne sakamakon faduwar da ya yi a kasuwannin duniya.

Tuni dai wannan mataki ya yi wa wasu ‘yan Najeriya dadi, inda a bangare guda kuma bai yiwa wasu dadi ba saboda suna ganin da zarar komai zama lafiya a kasashen duniya, sakamakon cutar Coronavirus.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: