Majalisa ta amince da cin bashin $5.5bn da Buhari zai yi

A ranar Talata majalisar dattijai ta amince da bashin $5.5bn da Buhari zai ciyo daga kasar waje. Shugaba Buhari ya aika da wasika a ranar 10 Oktoba yana neman amintar su don ya ciwo bashin. Buhari ya ce bashin da zai ciwo za’a yi amfani da shi ne wajen cikasa kasafin kudin 2017 sannan kuma ayi amfani da ragowar a biya wasu basussukan da ake bin Najeriya wadanda lokacin biyan su ya yi.

Da farko sun ki yarda, sai da ya aika musu da Kwamitin cin bashi na kasa, wanda har da ministan sufuri, Rotimi Ameachi, suka je majalisa a ranar 19 Oktoba suka yi musu bayanin bukatar wannan bashi da Najeriya ke yi

Shehu Sani, Kaduna-APC, wanda har da shi a kwamitin cin bashin, ya ce bashin zai bude kafofin bunkasa tattalin arziki kuma zai samar da aiyukan yi ga al’ummar Najeriya, saboda har kamfaninnika masu zaman kan su zasu iya zuwa a basu bashi.

You might also like More from author

Comments are closed.