Majalisa ta baiwa Buhari sa’o’i 48 don yin bayani kan kisan gillar da akeyi a Najeriya

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari  sa’o’i 48 don yi wa ‘yan Najeriya bayani game da shirin da Gwamnati  ta ke yi wajen ganin an dakile kisan gillar mutanen  da ake yi a sassan jahohin Najeriya , da kuma  hukunta dukkanin wayanda aka kama da laifi aikata hakan a  kasar ta Najeriya.

Yan majalisar sun bukaci fadar shugaban kasa, hafsoshin tsaro, ministan tsaro, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya da dai sauran masu fada aji na kasar, akan yanda za’a  kawu   hanyar magance yawan kisan- gillar da ‘yan bindiga, masa garkuwa da mutane da kuma barayi ke yi a kasar  ta Najeriya tare da yi musu hukuncin da ya kamata.

You might also like More from author

Comments are closed.