Majalisar Za Ta Fara Muhawara Kan Kasafin Kudin 2019 Ranar Laraba

Shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya ce majalisar za ta fara muhawara kan kasafin kudin shekarar 2019 a ranar Larabar gobe, Sarakin ya bayyana hakan ne a zaman da majalisar ta yi yau Talata, sannan za a kare muhawarar a ranar 19 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Ya bukaci ilahirin ‘yan majalisar su sanya sunayensu a rijistar majalisar don samun damar bada gudummuwa a lokacin da za a gudanar da muhawarar, an dage muhawara akan kasafin kudin ne sakamakon hutun kirsemeti, sannan aka sake dagewa saboda manyan zabukkan da aka gudanar.

Kasafin kudin wannan shekarar ta 2019, ya kai Naira tiriliyan 8.73, shugaban kasa Buhari ne ya gabatar da kasafin ga majalisun wakilai da na dattawa a ranar 19 ga watan Disamban shekarar 2018.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: