Majalsa ta amince da kasafi kudi na INEC biliyan 189.2

Kwamitin Hadin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya dake kula da harkokin zabe ta amince a bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, naira biliyan 143 daga cikin kudade naira biliyan 189.2 da ta nemi a ba ta domin gudanar da zaben 2019.
yayin da bukatar ta hukumar ta INEC ta isa majalisa tun a watan yuli, duba da shafe makonnin da akayi wurin tattauna batun kudaden zauren kwamitin majalisar.

A wasikar da Shugaba Buhari ya aika Majalisar Dattawa, ya ce INEC zata karbi naira biliyan 189.2 don gudanar zaben na 2019, amma a fara bai wa hukumar naira biliyan 143.5 a daga cikin wannan shekara, naira biliyan 45.6 kuma ta biyu baya a shekarar 2019 mai gabatowa a nan kusa.

Sai dai Shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bukaci da a basu kudaden a dukule wuri guda batare an kasafta su.
Dahaka kwamitin ya bayyana amincewar bawa INEC naira biliyan 143 daga cikin kudi, bayan gama gudanar da taro na tattaunawa a kai.
Yayin da suka amince da matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na cewa a fara bayar da naira biliyan 143 daga cikin kudin a shekara da muke ciki ta 2018.

You might also like More from author

Comments are closed.