Majilisar dattawa ta tabbatar da Tanko a matsayin Alkalin alkalai

Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da Alkalin-alkalan Najeriya wato  Ibrahim Tanko Mohammed, a matsayin tabbataccen shugaban alkalan Najeriya a yau Laraba17 ga watan Yuli 2019.

A ranar Alhamis din data wuce ne, shugaba Buhari ya aike da wasika zuwa majalisar dattawa Najeriya, inda ya bukaci yan majalisar su tabbatar da Tanko Muhammad a matsayin shugaban Alkalan Najeriya na dindin-din. Wannan ya biyo bayan takardar majalisar koli ta shari’a wacce ta bukaci Buhari ya tabbatar da Tanko Mohammad a mataayin cikakken Alkalin-Alkalai.

Shugaba Buhari ya nada mai shari’a Tanko Mohammad a watan Junairu bayan dakatar da tsohon Alkalin-alkalai, Walter Onnoghen, wanda aka tuhuma da zargin boye kadarorinsa.

An haifi mai shari’a Tanko a ranar 31 ga Disamba, 1953 a Doguwa, karamar hukumar Giade  dake arewacin Jahar Bauchi.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: