Martani gwamna Ganduje ga Bidiyon cin hanci

Gwamnan jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce yada bidiyon da ake yi na zarginsa yana karbar kudin rashawa daga ‘yan kwangila da ba’a zan suwaya b aba ba zai hana shi sumun nasarar lashe  zabe mai gabaotawa na  2019 ba.

Ganduje ya ce wasu ‘yan hamayya sun dogara wajen yada bidiyon zargin karbar kudaden a matsayin hanyar da za ta kai su ga cin zabe.

Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da yake magana da wasu ‘yan kasuwa a fadar gwamnatin ta Kano.

Hakan ya zama karon na farko da  Gwamnan  Ganduje ya yi magana a fili kan batun bidiyoyin da ake yadawa na zargin karbar kudade daga ‘yan kwangila.

“Suna nan suna jira za su ci zabe a bidiyo,” a cewar Ganduje a lokacin da ake yi masa sowa da tafi.

Ya yi zargin cewa bokan masu hamayya da shi ne ya fada musu cewa za su yi nasara a zaben, tun da akwai bidiyon zargin karbar cin hanci.

Sai gwamna Ganduje bai ambaci sunan mutanen  da yake zargi suna amfani da bidiyon domin cimma manufar siyasa ba

Sai  kamar yanda aksan akwai zazzafar hamayyar siyasa tsakaninsa da ‘yan PDP musamman bangaren tsohon gwamnan jahar Rabiu Musa Kwamkwaso.

 

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.