Martani Kwankwaso ga Bidiyon Gwamna Ganduje

Tsohon gwamnan Jahar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce ya yi yunkurin ganin ba a fitar da bidiyon da ya yi zargin nuna gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje yana karbar cin hanci daga wurin ‘yan kwangila.

A cewar sa, “Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi, saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri.”

Dan majalisar dattawan ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan rediyon Dala FM da ke jahar ta Kano.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda abin da ake zargin gwamnan jahar da aikatawa.

Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya rikida ya koma makiyi.

Kwankwaso  ya sha alwashin yin aiki tukuru wajen ganin an sauya gwamnatin

 

You might also like More from author

Comments are closed.