Maryam Sanda ta daukaka kara a kotu bisa hukuncin kisa a ka yanke mata

Maryam Sanda ta daukaka kara a babbar Kotun Daukaka Kara da ke birnin Abuja, bisa dalilin kalubalantar hukuncin da aka yanke mata na kisa, sakamakon samun ta da laifin kashe mijinta, wanda babbar kotu ta yi.

A watan Nuwamban 2017 aka zarge ta da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Haliru Bello.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Maryam ta daukaka karar ne a ranar Alhamis, mako uku bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mata hukuncin kisa kan laifin kashe mijinta.

 

BBC ta rawaito cewa a takardar daukaka karar da ta rubuta wa kotun kan dalilai 20, Maryam, ta bukaci kotun daukaka karar ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a kanta.

Ta yi zargin cewa alkalin kotun Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yi hukuncin bisa son rai.

A cewarta hakan ya jawo danne ‘yancinta na samun adalci da kuma yanke mata hukunci bisa amfani da hujja ta zahiri.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: