Masu Garkuwa Da Mutane Sun Bukaci Miliyan 300 Don Sakin Mal. Ahmad Sulaiman

Rahotanni na bayyana cewa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shaharran malamin nan makarancin Al’Qur’ani Sheikh Ahmad Sulaiman da wasu mutane 5 a hanyarsu ta dawowarsu daga jahar Kebbi, a tsakanin kauyen Sheme da Kankara ta jahar Katsina, a daren Alhamis.

Sai dai  a cikin wani faifan odiyo dake zagaya wa kasar ta Najeriya na nu cewa masu garkuwar sun ce babban dan siyasa ne ya sa su suka biyo shi  daga Birnin Kebbi kuma suka zamu nasara kama shi, sannan sun basu miliyan 300 kafin suyi yankurin kama shi.

Hakan yasa masu garkuwar suka ce suna bukatar miliyan 300 tare da kudin mai daga bagaren Sheikh Ahmad Sulaiman dan mayar wa da wayan can kudin su.

Shin wa kuke ganin a kasar Najeriya ya cancanci bayar da wannan makudan kudaden?.Dan kubutar da Sheikh Ahmad Sulaiman ko kuna ganin bincike ya kamata a gudanar dan kama mutanen da suka yi garkuwa da Malamin.?

 

You might also like More from author

Comments are closed.