Matsalar fyade: Yan sanda na  bincike don gano ranakun da aka fi yin fyade a Kano

Rundunar kwamishinan ‘yan Kano Habu Sani ta ce zuwa yanzu ta kama mutum 50 bisa zargin aikata fyade.
Rudunar yan sanda a Kano ta ce wani bincikenta ya gano cewa kashi daya cikin uku na illahirin laifukan fyaden da ake aikatawa cikin unguwannin jahar, a kangwaye ake yin su.

Mun kuma gano cewa mafi yawan waɗanda ake yi wa fyade din nan, sama da kashi 40 ana musu fyade ne bayan an yaudare su da kudi ko abinci,” in ji jami’in dan sandan.

Ta ce don haka za ta fara kama masu irin wadanan kangwaye da suka gano an aikata fyade don tuhumarsu da taimakawa wajen aikata laifi.

“Mafi yawancin fyaden da ake yi, a kangwaye ake yin su” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan. “Kimanin kashi 33.3% na duk fyaden da aka yi a Kano”.

BBC ta rawaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kashi 20.8% na fyaden da suka yi bincike kansu, an aikata su ne a gonaki da burtalai, Yayin da kashi 16.7% na fyaden a gidan wadanda aka yi wa cin zarafin aka aikata su.

A cewar jami’in dan sandan daga watan Janairun 2020 zuwa yanzu, rundunar ta karbi korafe-korafe kan aikata fyade guda 45, kuma tuni sun kama wasu da suke zargi har ma an gurfanar da su a gaban kotuna.

Abdullahi Haruna ya ce daga cikin mutanen, tuni kotu ta samu 27 da laifi, inda ta yanke musu hukuncin da ya hadar da dauri har na tsawon shekara 14 da biyan diyya ga wadanda aka yi fyaden.

Ya kuma ce suna ci gaba da gudanar da binciken, don tantance ƙaruwa ko raguwar aikata fyade baya-bayan nan a cikin jahar Kano.

“Yanzu binciken namu ma har ya kai, muna bibiyar waɗanne ranaku ne da awoyi aka fi yin wadannan laifuka na fyade.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: