Matsalar rashin wuta ta addabi jama’a

Duk da cewar yanayi na zafi ya dauki sawu
a yawancin kasashen Afirka da ke yankin
kudu da Sahara, matsalar klarancin wutar
lantari na ci gaba da damun jama’a
musamman masu sanao’i.

Wannan matsalar daukewar wutar lantarkin
dai ta saka al’umma cikin tarin matsaloli
game da al’amuran rayuwarsu ta yau da
kullum inda har jama’a suka fara kwana a
bakin panpuna wajen neman ruwa.

Tuni dai jama’a suka fara bayyana
fargabarsu da wannan matsala game da
yadda zasu kasance tare da ita a cikin
watan azumin Ramadan.

 

Wannan matsala ta karancin ruwa ta fara
tsamari ne kamar yadda wasu daga cikin
mazauna unguwannin kan tudu suka koka.
Inda suke kwashe fiye da rabin sao’in dare
ba tare da ko iska ta zo a pampunan su ba
matsalar da a cewar su a shekarun baya
hukumomi ke daukan ta a zaman tarifi a
wanan birni da kewaye.

A yanzu haka dai al’ummar birnin na
Damagaram ta haura a ganga dubu 24 inda
kuma a kan samu tarin jarkoki a pompunan
kan layi a wurare daban daban, da suke
shiga layi ko da ruwa yazo cikin dare yayin
da wasu unguwannin basu ma san da ko
ana wuyar ruwa ba.

You might also like More from author

Comments are closed.