Mutuwar  sanata Longjan majalisa ta dage zama zuwa gobe

Majalisar dattawan Najeriya ta dage zaman zauren majalisar zuwa gobe Raraba 12 ga watan fabrairu 2020 sakamakon mutuwar sanata Longjan

Sanata mai wakiltar Plateau ta kudu wato Ignatius Longjan ya mutu ne a a asibitin Turkiyya dake Abuja a ranar Lahadi,ya muta yana  da shekaru 75 a duniya.

Sanata Yahaya Abdullahi, ya gabatar da hakan ne a zauren majalisa kuma shugaban marasa rinjaye, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya amince da hakan.

Mataimakin shugaban majalisa sanata Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar  na yau, ya sanar da cewa gobe za’a karrama marigayi sanata Benjamin Uwajumogu, wanda ya mutu a Disamba, 2019.

Omo-Agege ya yi kira ga abokan aikinsa su sanya farin kaya ko baki gobe.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: