Obasanjo na bukatar a duba lafiyar sa – Buhari
Gwamnatin Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan wasikar da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya fitar wadda a ciki ya soki lamirin gwamnatin.
Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani a kan wasikar da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a kan mulkin gwamnati mai ci gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe a watan gobe.
Kakakin ya bayyana wasikar da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a matsayin wani yunkurin wasu ‘yan siyasa da ba za su iya ja da Shugaba Buhari ba a siyasance sai dai su rika cin dunduniyarsa shi ne kawai abun da zasu iya yi.
Sanarwar na cewa da alama tsohon shugaban kasar na bukatar kwararren likita daya duba shi dan tabbatar da lafiyarsa, tare da bashi shawarar ya nemin likita da gaggawa.
Sannan kuma yayi masa fatan samun waraka cikin sauri, tare dayi masa addu’ar Allah ya bashi lafiya.
Comments are closed.