Orji Kalu zai cigaba da karbar albashi da alawus kamar kowanne sanata – Majalisar Dattawa

 

Sanata Orji Kalu wanda yanzu haka ya ke gidan yari zai ci gaba da karbar albashi da sauran hakkokinsa kamar kowanne sanata.
Mai magana da yawun majalisar dattawan kasar, Sanata Godiya Akwashiki ne ya bayyana wa jaridar PREMIUM TIMES ranar Lahadi 8 ga wata Disamba 2019.
Sanata Akwashiki ya kara da cewa duk da an samu mista Orji Kalu da laifi kuma an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso, har yanzu sanata ne kuma zai ci gaba da karbar albashi da sauran hakkokinsa.

Ya kara da cewa idan dai har ba kotun koli ce ta yanke hukuncin karshe ba kan dan majalisar dattawan ba to Orji zai ci gaba da kasancewa sanata.
Sai dai kuma mai magana da yawun majalisar ya ce kasancewar Orji Kalu sanata ba ya na nufin zai rinka halartar zaman zauren majalisar ba.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: