Rashin sanin tsaro yasa wasu ke ganin jami’an tsaro basuyin kokari – Buratai

Babban hafsin sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya yi magana game da kashe-kashen da ke faruwa a jahar Zamfara.

A bidiyo da BBC Hausa ta saka a safin ta  wanda ake tambayar shi kan cewa ana ganin wasu sojojin sun gaza bisa la’akari da cewa ana garkuwa da mutane duba da  cewa sun na fadin mutukar kakarin da suke game a al’amarin.

Buratai  yace duk  wanda ya ce sojojin Najeriya  ba suyin  kokari ta bai san sha’anin menene tsaro ba.

Ya kara da cewa shi tsaro ana fara shi ne daga matakin fako – wato daga kan jama’a.

A karshe ya  bayyana cewar sojoji na yin iya  bakin kokarinsu wajen ganin sun tabbatar kare rayukan al’umar  kasarta Najeriya ga baki daya.

 

You might also like More from author

Comments are closed.