Sai na Kori Wenger idan na sayi ARSENAL –Dangote

Aliko Dangote yace abin farko da zai yi idan ya sayi Club din Arsenal shine ya sallami Arsen Wenger a matsayin mai horas da Kungiyar

A tattaunawar da akayi dashi a interview with Bloomberg Dangote wanda

Yafi kowa kudi a nahiyar Afrika, masoyin club din Arsenal ne tun a shekara ta 1980, ya jaddada kudurin sa na sake neman tayin zuba hannun jari a kungiyar wasan yayin da yakammala matatar man fetur da yake ginawa a Ikko, Lagos kimanin dala biliyan goma sha daya $11

“Abin farko da zanyi shine a canja mai horas wa a kungiyar, Wenger yayi matukar kokari amman yakamata wani shima yagwada damarsa” Dangote

Arsen Wenger shine mafi jimawar ma ihoras wa a yanzu, tun 1996, ya samu nasarar lashe kofin zakaru na Ingilahar sau uku da kuma FA Cup sau bakwai. A watan Mayu yakara rattaba hannun kan kwantaragin tsayawar sa a Kungiyar kallon kafa ta Arsenal

You might also like More from author

Comments are closed.