Sanata 1 ya kamaci kowacce jahar – Rochas

Menene ra’ayin ku game da hakan?
Sanata mai wakiltar jahar Imo ta yamma Rochas Okorocha ya yi kira a rage yawan yan majalisar dokokin kasar Najeriya dan kawo karshen kashe kudin da gwamnati take yin a babu gaira babu dalili, a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba 2019, a zauren majalisar.
 
Rochas yace tsarin mulkin Najeriya ya bukaci samar da sanatoci 3 a kowacce jahar, amma hakan bata kudi ne. Sanata 1 ya kamata a samar a kowacce jahar sanatocin dayawa mene amfanin su?
 
Ban san me muke yi ba wanda ya banbanta da wanda aka gudanar a majalisa ta 8, majalisa ta 7, majalisa ta 6 da ma dai sauran su.
Abunda muke yi a yanzu kusan abu daya ne dana majalisa ta 8, kuma ina mai tabbatar muku da cewa idan aka cigaba a hakan to babu wani abu da zai chaja. Inji shi.
 
A yanzu dai sanatoci 109 ne a majalisar dattawan, yan majalisar dokokin tarayya kuma guda 360 a kasar ta Najeriya

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: