Sanata Shehu Sani ya fusata kan watsi da aka yi da mutanen da aka kai ma hari a Birnin Gwari

Sanata Shehu Sani ya fusata kan watsi da aka yi da mutanen da aka kai ma hari a Birnin Gwari

Shehu Sani ya bayyana haka ne a zaman majalisa na ranar Talata 6 ga watan Feburairu, inda ya zargi gwamnati da kuma hukumomin tsaron gwamnatin da nuna halin rashin damuwa da ayyukan yan bindigan a jihar Kaduna

Sanatan ya bayyana ma majalisar dattawa cewa ayyukan sace sacen mutane, fashi da Makai da garkuwa da mutane ya zama ruwna dare a jihar Kaduna, amma duk da haka gwmnatin tarayya bata nuna damuwarta na magance matsalar ba.

“Na damu kwarai da gaske da yadda gwamnatin tarayya bata iya tabbatar da tsaron yan Najeriya, balle mana dukiyoyinsum gwamnati ta gaza. “Abin kunya ne ace bayan sama da shekaru 100 da samar da Najeriya amma yan Najeriya basa iya zama cikin tsaro a kasarsu, amma kasashen Kamaru, Nijar da Bini duk suna da ingantaccen tsaro. Don haka ina kira ga duk wanda lamarin ya shafa da su mayar da hankalinsu kan matsalar.” Inji shi.

You might also like More from author

Comments are closed.