Saraki Ya Dauki Nauyin Wani Gagarumin Fim Din Hausa Kan Naira Miliyan 36

Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, ya dauki nauyin wani gagarumin fim din Hausa mai suna ‘Mutum Da Addininsa’ a kan kudi Naira miliyan 36, don kawo karshen rikicin kabilanci da bambance-bambancen addini.

Fim din, wanda kamfani Chali Enterprises ya dauki nauyi, ya kunshi babban mashahurin jarumin Kannywood din nan, Ali Nuhu, shi ne ya jagoranci jaruman da ke cikin fim din, sannan fitaccen mai shiryawa Naziru Danhajiya ne ya shirya shi.

A wata tattaunawa da mu ka yi da shugaban kamfanin Chali, wato Alhaji Salisu Aliyu Chali, ya bayyana ma na cewa, Bukola Saraki ya dauki nauyin fim din ne, saboda ya kunshi batun addini da jin kai da kuma almajiranci a kasar Hausa da Najeriya bakidaya.

Chali, wanda shi ma jarumi ne mai fitowa a finafinai jifa-jifa kuma mai shiryawa, sannan dan kasuwa ya kara da cewa, “Mutum Da Addininsa ya kuma tabo batun taimaka wa na kasa, domin kai ma Allah Ya biya ma ka taka bukatar.

Wadannan ne dalilan da su ka sa Mai girma Sanata Bukola Saraki ya dauki nauyin fim din, saboda halin da kasar nan ta ke ciki na kashe-kashe da kabilanci a Najeriya kan bambancin addinai.” Shi ma daya daga cikin ’yan kwamitin kaddamar da fim din na Mutum Da Addininsa, Magaji Maikarama, ya bayyana ma na cewa, an je akalla jihohi da dama a lokacin daukar shirin, wadanda su ka hada da Edo, Lagos, Neja, Kano, Filato, Kaduna da Abuja.

Daga LeaderShip Hausa

 

You might also like More from author

Comments are closed.