Shin koh menene dalilin da yasa Atiku ya zabi Sokoto gurin kaddamar da kamfen ?

Dan takarar shugaban kasa Najeriya karkashinta inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar ta kamfen din tsayawa takarar a jahar Sokoto da ke arewa maso gabashin Najeriya , a ranar Litinin 3 ga watan Disamba 2018.
Hakan ya sa kamfen din ya zama na farko a gurin Atiku Abubakar a kasar Najeriya.

Jam’iyyar PDP dai itace ta zabi fara kamfen din a jihar Sokoto ne saboda Jam’iyyar tayi amfani da gangamin don ganawa da shugabannin al’umma dake yanki, don ci gaba da tattaunawa don neman hadin kansu wajen “ceto kasar daga rashin iya shugabanci na Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gazawar APC,” a cewar yan jam’iyyar ta PDP.

You might also like More from author

Comments are closed.