Shugaba Buhari na gab da gabatar da kasafin kudi na 2020 a Majalisa

Majalisar tarayya ta kasar Najeriya ta fitar da Talata 8 ga watan Oktoba a matsayin ranar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a gaban yan majalisa.
 
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da wannan ta bakinshugaban majalisa wato Lawal Ahmed Sanatocin a yau Alhamis, 3 ga Watan Oktoban 2019.
 
Sanata Adedayo Adeyeye ya shaidawa Manema labarai cewa shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana a gabansu ne da kundin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2020 a makon gobe.
 
Kamar yadda aka saba a Najeriya, yan majalisar wakilai da Takwarorinsu na dattawa za su karbi shugaba Buhari a babban zauren majalisar Najeriya da ke babban birnin tarayya na Abuja.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: