Shugaban Buhari ya mika sakon Ta’aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Tony Anenih
Tsohon ministan Ayyuka,Tony Anenih ya rasu yana da shekaru 85, ya rasu a yau Litinin 29 ga watan Oktoba a asibitin Cedarcrest Hospital dake babban birnin tarayya Abuja, bayan ya sha fama da rashin lafiya , sai dai ba’a bayyana abunda yake damunsa ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigayi tsohon ministan Ayyuka Tony Anenih , tare da jajanta musu.
Inda yakara da cewar Najeriya ta yi rashin gwarzo kuma hazikin dan kasa.
Comments are closed.