Tsokacin da Jami’yyun siyasar Najeriya suka yi wa INEC kan kudin zabe

Ra’ayin Jam’iyyun siyasar yan  Najeriya ya bambamta  kan kalaman da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, na  cewar za ta yi amfani da wasu hanyoyi domin bin diddigin kudaden da jam’iyyun siyasa ke kashewa, a lokacin yakin neman zabe.

Hakan ya zamo abun mamaki ga Babbar jam’iyyar adawa  PDP, saida kuma jam’iyyar tace hukumar zaben ta yi duba bisa adalci akai, inda suka kara da cewa

“Jam’iyyarsu  ba ta da kudi, kuma bata da  gwamnati saboda haka dan  gwargwadon abin da suke kasuwanci shi suka tattara gurin yin zaben .

Ita kuwa jam’iyyar ta APC mai mulki ta ce matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi daidai,  saboda ta hakan za’a iya bambance  tsakanin aya da tsakuwa.

You might also like More from author

Comments are closed.