Wasannin Kwallon Kafa

Real Madrid za ta duba yiwuwar sayar da dan wasan gaban kasar Wales Gareth Bale a karshen kakar wasan da muke ciki – ko kuma a bayar da aron dan wasan mai shekaru 29 in ba a sami kungiyar da ta nuna sha’awar sayen dan wasan ba, in ji Marca.

Da yiwuwar Bale ka iya komawa Manchester United a matsayin aro
kan kudin da ba zai wuce fam miliyan £5m, a cewar jaridar Mirror.

Golan kasar Spain David de Gea,mai shekaru 28, da dan wasan tsakiyar kasar Faransa Paul Pogba, mai shekaru26, dan wasan gaban kasar Belgium Romelu Lukaku,mai shekaru 25, dukaninsu za su tunani akan makomarsu idan Manchester United ta gaza samun gurbin doka gasar Zakarun Turai ta Champions League, in ji jaridar Guardian.

Manchester City ta shirya karya tarihinta na sayen dan wasa mafi tsada a kungiyar da shirin da take yi na daukar dan wasan kasar Spain Rodri, mai shekaru 22, daga Atletico
Madrid don ya zama dan wasan da zai maye gurbin dan wasan tsakiyar kasar Brazil Fernandinho,mai shekaru 33, in ji Telegraph.

Juventus ta shirya wajen kalu-balantar Tottenham
a karshen wannan kakar wasan wajen zawarcin matashin dan wasan Fulham back Ryan Sessegnon, mai shekaru 18, a cewar Express.

Unai Emery zai yi kwalemar wasu daga cikin yan wasan Arsenal a karshen kakar wasan nan
-inda dan wasan bayan kasar Jamus Shkodran Mustafi,mai shekaru 27, ke cikin yan wasan da za sayar, a cewar jaridar Mail.

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya yi imani da cewa kocin Nice Patrick Vieira, mai shekaru 42, wanda tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal ne, ya nu dukanin wasu alamu na kwarewa da zai zama kocin Gunners din a nan gaba, in ji Times.

Ana tsammanin Barcelona za ta wa dan wasan tsakiyar kasar Chile Arturo Vidal, mai shekaru 31, tayin tsawaita Kwantiragensa na tsawon shekara daya
kan kwantiragensa, wadda za ta kare a 2021, a cewar Sport.

Tsohon kocin Manchester United David
Moyes ya ce bai yi imani da cewa kulob din zai kare cikin jerin kungiyoyi hudu na saman tebur ba, a wannan kakar wasan, in ji jaridar Sun

You might also like More from author

Comments are closed.