Wayanda suka sauya sheka daga APC zuwa PDP suna ganin hukuncin – Oshoimhole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, ya yi jawabi a kan yan siyasar da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP,ciki har tsohon shugaban majalisar dattawa wato Bukola Saraki.

Adams Oshiomhole ya bayyana cewa mutanen Najeriya sun hukunta yan majalisa da aka zaba karkashin jam’iyyar APC, kuma suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a tsakiyar shekarar 2018.

Ya bayyana hakkan ne a fadar shugaban kasa a ranar litinin 18 ga watan Nuwamba 2019, lokacin da ya jagoranci Jiga-jigan APC wajen gabatar da sabon gwamnan APC mai jiran-gado. Inda ya kara da cewa, Dino Melaye kadai ya rage yanzu, cikin wayanda su ka sauya-sheka daga APC kafin zaben 2019.

Sai dai shi kadai ya iya rike kujerarsa, yayin daga baya kuma kotu ta soke zaben tare da bukatar a gudanar da wani sabon zaben.

An fafata da Dino Melaye da Smart Adeyami a zaben, kuma yadda zaben ya wakana, Smart ya bawa Dino ratar Kuri’u 20,000 duk da cewa INEC ta ce zaben bai kammalu ba tukun.

Oshiomhole yace su na da yakinin cewa babu yadda za ayi Sanata Dino Melaye ya kamo tazarar kuri’u 20, 000 da dan takarar APC ya ba shi a zaben.

Ina tunanin ya zama mana darasi mu sani cewa idan yan siyasa su ka yi takara a wata jam’iyya, sai kuma su ka yi watsi da wannan jam’iyyar da ta kawo su, masu zabe su na nan za su jira su.Inji shi

Sanatocin da su ka bar APC a watan Yulin 2018 sun hada dakta Rabi’u Kwankwaso na jahar Kano, Barnabas Gemade na jahar Benue, Suleiman Hunkuyi na jahar Kaduna , Shaaba Lafiagi na jahar Kwara, Isa Hamma Misau na jahar Bauchi, Usman Nafada na jahar Gombe da kuma Suleiman Nazif na jahar Bauchi.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: