Yadda Omo-Agege ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa

Sanata Omo-Agege na jam’iyyar APC ya lashe zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa, inda ya doke Sanata Ike Ekweremadu na jam’iyyar PDP.

Sanatoci 105 ne suka kada kuri’a a zaben mataimakin shugaba – daya ya kaura ce – yayin da kuri’a daya kuma ta lalace.

Omo-Agege ya samu kuri’u 68 yayin da Sanata Ike Ekweremadu ya samu 37.

Tun da farko an zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Ike Ekweremadu shi ne tsohon mataimakin shugaban majalisar, inda ya shafe shekara 12 a kan mukamin.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: