Yadda sojojin Najeriya suka tarwatsa sansanin Boko Haram a dajin sambisa

Rundunar sojojin saman Najeriya karkashin dakarun Operation Lafiya Dole, sun sanar da cewa sun gano maboyar yan Boko Haram a dajin na Sambisa da ke jahar Borno.Hakkan yasa suke gudanar da taron tattaunawa.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce dakarun sun samu nasarar tarwatsa sansanin mayakan ne ta hanyar samun wasu bayanan sirri a ranar Lahadi 13 ga watan Oktoba 2019.

Ibikunle, ya kara da cewa sansanin mayakan ya kasance waje ne  da Kwamandojin kungiyar ke zuwa don bayar da umarnin kai hari ga fararen hula.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: