Yadda ta kaya da Shehu Sani a kotu yau

Shari’ar Shehu Sani: Sowore ya bayyana a kotu, sai dai bai iso kotun da wuri ba, sai da alkali ya zauna tukunna.

Ma’aikatan Bankin Guarantee Trust  wato (GTB)Beckley Ojo da Elizabeth Nwoka sun bayyana  a gaban wata babbar kotun Najeriya da ke babban birnin Abuja a yau Talata 25 ga watan Fabrairu, dan bada shaida a kan  shari’ar tsohon dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, wato Shehu Sani.

Beckley Ojo da Elizabeth Nwoka sun bayyana a gaban kotun karkashin shugabancin Alkali mai shari’a Inyang Ekwo dan bada shaida, shaidun sun bayyana wa kotu cewa, an sanya kudi naira miliyam 3.5 a asusun bankin  Zailani Shanono  dake tare da kamfanin motocin ASD  ta hanyar takardar bankin GT.

Shaidun sun bayyana wa kotun cewa,  baisu da masaniya kan  wanda ake tuhumar domin basu taba ido da ido da suba ba, inda suka nuna  ba hurumta bane,  yayin da aka musa  tambayar, shin wanda ake tuhumar shine mai asusun banki da akayi mu’amula wajen sanya kudaden a asusun bankin na Zailani.

Sannan Elizabeth Nwoka ta kara da cewa an fitar da naira miliyan biyar(5m) daga  cikin assusun kamfanin motocin ASD zuwa bankin  mista Abubakar Mohammad

Hukumar  EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a gaban wata babbar kotun da ke zamanta a Abuja bisa zargin zamba cikin aminci na dala 25,000, inda kotun ta bayar da belinsa.

Shehu Sani ya musanta zargin da EFCC ke masa na karbar kudin daga hannun wani  Sani Dauda, dillalin motoci.

A karshe kotun karkashin shugabancin Alkali Inyang Ekwota ta dage zaman zuwa gobe 26 ga watan Fabrairu dan cigaban sauraron shari’ar.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: