Yar Afirka lashe gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya

Fiye da mata 90 ne daga kasashe daban-daban suka fafata a gasar ta miss Universe.

Zozibini Tunzi yar kasar Afirka ta Kudu ce wacce ke da shekaru 26 ta samu nasarar lashe gasar Miss Universe da aka gudanar a birnin Atlanta dake kasar Amurka a ranar Litinin.

Sabuwar sarauniyar ta ce lokaci ya yi da za a daina kallon bakaken mata da kuma masu gashi irin na ta a matsayin munana mata.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: