Yusuf Buhari ya samu lafiya

Yusuf Buhari ya samu sauki garau har ya dawo gida daga asibiti bayan ya yi jinyar raunin da ya samu a hadarin da ya yi da babur.

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Muhammadu Buhari ce ta sanar da hakan a shafinta da sadar da zumunta na facebook mai suna Aisha Muhammadu Buhari, inda ta yi godiya ga Allah da Ya sa dansu ya dawo gida bayan gama jinyar.

Sannan ta yi godiya ga dumbin wadanda suka taya su addu’a bayan Yusuf ya yi hadarin.

Daga cikin wadanda suka tarbi Yusuf Buhari akwai Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau, da matar Mataimakin Shugaban Kasa da Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da Minista a ma’aikatan lafiya Dokta Osagie da sauran abokanan arziki.

You might also like More from author

Comments are closed.