Zaben Edo: Gwamna  Ganduji ne  zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da gwamnan Kano,  Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben na jahar Edo, wanda ake sa ran  gudanarwa a ranar 19 ga watan Satumba 2020.

 Sanarwar  da jam’iyyar  ta fitar mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai na kasa, Yekini Nabena, na cewa, kwamitin — mai kunshe da mambobin 49,  zai yi aike wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar.

Gwamnan jahar Imo Senata Hope Uzodima ne zai kasance mataimakin Ganduje,  Honourable Abbas Braimoh a matsayin sakataren kwamintin yakin neman zaben, inda tsoffin shugaban jam’iyyar  APC ta kasa, Adams Oshiomhole tare da John Odigie-Oyegun suna suna daga cikin membobin kwamitin.

An kafa kwimitin ne bayan amincewar shugaban na riko wato gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni a zaben da ake sa.

Jam’iyyar zata kaddamar da kwamitin, soma aikin, a ranar 6 ga watan Yuli 2020, a shedikwatar APC dake babban birnin tarayyar Abuja.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: