Zan karashe ayyukan da toshon gwamna Gaidam ya bari – Mai Mala Buni

Gwaman jahar Yobe, Mai Mala Buni ya kai ziyarar gani da ido a filin Jirgin da ake ginawa a babban birnin jahar wato Damaturu.

Mai Mala ya bayyana wa yan ma nema labarai  cewa, Gwamnatin shi za ta karasa dukkanin aiyukan da Gwamnati tsohon gwamnan jahar Ibrahim Gaidam ba ta kammala ba, kuma za su inganta wanda aka yi kamar yadda ya alkawarawa Talakawa lokacin da suke yakin neman zaben na 2019.

Gwaman Mai Mala yayi kira ga yan kwangila da su yi amfani da nagartattun kayan aiki masu kwari kamar yadda sukayi yarjejeniya da Gwamnati, sanan kuma  su kokari hanzartawa wajen kammala aikin na su.

 

Sakataren ma’aikatan Ayyukan jahar Yobe, Malam Abdullahi  Jawa yace, aikin gina filin jirgin yakai matakin kaso hamzin da biyar (55%) na kammalawa.

 

You might also like More from author

Comments are closed.